Sojojin Isra’ila sun kame Falasdinawa 15 a samamen da suka kai cikin dare a wasu yankunan Zirrin Gaza da ta mamaye.
An shirya hare-haren ne a biranen Jenin da Tulkerim.
Sojojin Isra’ila, wadanda ke yawan kai samame gidajen Falasdinawa a Zirrin Gaza dake Gabashin Kudus,na yawan tsare Falasdinawa.
Daga cikin Falasdinawan da Isra'ila ke tsare dasu a wasu cibiyoyi sun hada har da mata da yara.
A gefe guda kuma, sojojin Isra’ila sun rusa wata makarantar yara ta Falasdinu a garin Takku dake karkashin gundumar Beytullahim.
Magajin garin Takku Teysir Abu Muferreh ya ce sojojin Isra’ila sun sassare wasu bishiyoyin 'ya'yan itacen citrus mallakar Falasdinawa.