Sojojin gwamnatin Siriya sun kashe fararen hula 4 a Idlib

Sojojin gwamnatin Siriya sun kashe fararen hula 4 a Idlib

Sojojin gwamnatin Siriya karkashin Bashar Al-Asad sun kai hari Idlib tare da kashe fararen hula 4 da suka hada da yara kanana 2.

Kungiyar Kare Fararen Hula ta White Helmets ta sanar da cewa, dakarun Asad sun kai hari da makami mai linzami kan wata mota da ke tafiya a kauyen Najiyya da ke gundumar Jisir Al-Shuur.

Fararen hula 4 da suka hada da yara kanana 2 sun mutu sakamakon harin.

Wasu yaran 2 da suka samu munanan raunuka na samun kulawa a asibiti.

 


News Source:   ()