An bayyana cewar sakamakon rikicin da ya barke a iyakan Azerbaijan da Armeniya sojojin Azerbaijan biyu sun yi shahada inda wasu biyar kuma suka raunana.
Ma'aikatar harkokin tsaron kasar Azerbaijan ta bayyana cewa ta dakatar da harin gurnati da sojojin Armeniya suka harba zuwa sansanin sojan Azerbaijan a yankin Tovuz.
Dakarun na Azerbaijan sun mayar da martani lamarin da ya sanya sojojin Armeniya ja da baya bayan sun samu rashi.
A rikicin dai dakarun Azerbaijan biyu sun yi shahada inda wasu biyar suka raunana.