Dakarun sojin Azabaijan sun shiga yankin Lachin da aka kubutar daga mamayar Armeniya bayan shekaru 28.
A karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta da Rasha ta jagoranci Azabaijan da Armeniya sanya hannu a kai a watan da ya gabata, sojojin Armeniya sun fice daga Kelbejer da Agdam, a yanzu kuma sun bar yankin Lachin.
A ranar 27 ga Satumba ne Azabaian ta fara kai farmakai inda ta kubutar da manyan garuruwa 5, kanana 4 da kauyuka 286 daga mamayar Armeniya, kuma Armeniya ta yi alkawarin janyewa daga garuruwan Agdam, Kelbejer da Lachin.
A ranar 20 ga Nuwamba sojojin Armeniya suka janye daga Agdam, a ranar 25ga watan kuma suka fice daga Kelbejer.