A shekarar 2019 da ta gabata sojojin Amurka 498 ne suka kashe kansu.
Rahoton da Ma'aikatar Tsaro ta Amurka Pentagon ta fitar ya bayyana cewar, daga cikin sojojin da suka kashe kawunansu akwai masu damara 344 sai sauran kuma da suke kanana sojoji.
Daga cikin sojojin akwai na kasa 142, na sama 83, na ruwa 72 sai wasu na musamman su 47.
Rahoton ya kuma ce a 2018 sojoji masu damara 326, a 2017 kuma 287 ne suka kashe kawunansu.