Sojin Isra'ila 130 sun aikewa gwamnati wasiƙar neman daina yaƙi a Gaza

Sojin Isra'ila 130 sun aikewa gwamnati wasiƙar neman daina yaƙi a Gaza

A wata wasikar da suka rubuta ta ranar 9 ga wannan watan, sojojin da wadanda aka kira domin yiwa kasar yaki sun ce sun fahimci gwamnatin kasar ba ta son kawo karshen yakin domin gudanar da zabe.

Daya daga cikin sojojin ya ce tun da babu wani ci gaba wajen kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su, saboda haka babu dalilin ci gaba da wannan yakin da kasar ke yi.

Sojan ya ce wannan wani matsayi ne ya dauka na bijirewa gwamnatin kasarsa saboda yadda ta kai matakin karshe na yaudara.

Sojan ya ce da da gaske ake yi wajen kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su, da tintini anyi nasara, amma ana tsawaita yakin ne domin kin gudanar da zabe, matakin da zai bai wa (firaminista) damar ci gaba da zama a karagar mulki.

Rahotanni sun ce wasikar ta harzuka gwamnati wadda ta dakatar da wasu daga cikin sojojin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)