An sanar da cewa harin ta'addanci da aka kai a yankin Idlib din kasar Siriya a ranar 5 ga watan Yuni sojan Turkiyya da ya samu munanan raunuka a ranar ya yi shahada.
Ma'aikatar Harkokin Tsaron Kasar Turkiyya ta shaidawa manema labarai cewa duk da iya fama da malaman lafiya suka yi akan sojan da ya sami munanan raunuka a harin ta'addanci da aka kaiwa sojojin Turkiyya a yankin Idlib din kasar Siriya, sojan ya rigamu gidan gaskiya.