An sanar da shahadar wani sojan Turkiyya a yayin farmakin kamborin damisa da dakarun kasar ke kaiwa a yankin Iraki.
Ma'aikatar tsaron kasar Turkiyya ta fitar da sanarwa a rubuce dake nuna cewa sanadiyar rikicin da 'yan ta'adda suka tayar a yankin Zap sojan da ya raunana wanda aka garzaya dashi asibiti ya rigamu gidan gaskiya.
Sanarwar ta kara da cewa an magance 'yan ta'addar PKK 4 a wata farmakin da aka kai ta sama a yankin.