Sojan Turkiyya 1 ya yi Shahada a iyakar kasar da Siriya

Sojan Turkiyya 1 ya yi Shahada a iyakar kasar da Siriya

A gundumar Kiziltepe da ke lardin Mardin, sojan Turkiyya 1 ya yi Shahada yayinda wasu 3 suka jikkata sakamakon bude wuta da aka yi daga kasar Siriya.

Sanarwar da Fadar Gwamnan Mardin ta fitar ta ce, an bude wuta daga cikin kasar Siriya kan motar sojoji da ke sintiri a iyakar Senyurt.

Sakamakon harsashi da ya samu direban motar Cihan Ciftcibasi ya sanya motar ta kife inda sojoi suka samu raunuka.

Duk yunkurin da aka yi a asibitin gwamnati na Kiziltepe an gaza ceton rayuwar Ciftcibasi inda ya yi Shahada.

Sauran sojoji 3 da suka jikkata na ci gaba da karbar magani a asibiti.


News Source:   ()