Gamman Siriyawa mazauna Turkiyya sun gudanar da zanga-zangar kalubalantar kwarya-kwaryar zaben da gwamnatin Bashar Asad ta shirya a kasar Siriya.
Siriyawan sun taru ne a gaban ofishin jakadan Siriya dake yankin Harbiye a birnin Istanbul inda suka yayyaga hotonun Bashar Asad inda kuma suka daga tutocin dake nuni da yin juya juhali a Siriya.
An yanke hukuncin gudanar da zabe a kasar duk da irin matsalar tsaro da kasar ke cigaba da fama dashi, wanda babu ko alamaun kawo karshensa a kuma liokacin da kusan Siriya miliyan 10 ke neman mafaka a wajen kasar a daidai lokacin da kuma kusan kashi 40 na kasar bai hannun gwamnatin kasar.
Sallah Fadil, wanda ya kirkiro kungiyar Syrian House a madadin kungiyar ya bayyana cewa zaben ya sabawa ka’idojin kasa da kasa.
"Ba mu yi amanna da wannan zaben ba kuma muma masu kakkausar suka akansa”
A ranar 18 ga watan Afirilu ne majalisar kasar ta bayyana ranar 26 ga watan Mayu a matsayan ranar da za’a guadnara da zaben shugaban kasa, wanda ake ganin zai baiwa Basha Asad damar cigaba da mülkin kasar dake fama da yakin basasa.
An yi hasashen cewa shugaban mai shekaru 55 zai samu gagarumin nasara a zaben da za’a gudanar a ranar 26 ga watan Mayu, wanda ‘yan sa ido akan harkokin zabe na kasa da kasa suka bayyana cewa ba zai kasance mai inganci ba.
Adadin mutanen da suka mutu a duniya sakamakon kamuwa da kwayar cutar COVID-19 na iya zama sau biyu ko sau uku fiye da ainihin mutum miliyan 3.4 da aka bayyana.
Ana hasashen cewa dai wadanda korona ta kashe zasu iya kaiwa sama da miliyan 8, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana.