A wa'adinsa na farko, shugaba Trump ya dinga takun saka da wasu shugabannin Turai musamman a bangaren kasuwanci da kuma biyan kudaden tafiyar da kungiyar kawancen tsaro ta NATO wanda wasu kasashe ke jan kafa a kai.
Shugabar gudanarwar kungiyar Ursula von der Leyen ta bayyana cewar manufarsu itace hada kai domin tinkarar matsalolin dake gaban su tare.
Shi kuwa shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce wannan lokaci ne na su a Turai domin daukar mataki mai karfi. Macron ya yi tamabyar cewar, za su zuba ido ne domin karanta tarihin yakin da Vladimir Putin ya kaddamar ko na zaben Amurka ko kuma zabin da mutane China suka yi?, maimakon tarihin da su zasu rubuta wajen jagorancin yankin.
Watanni kafin gudanar da zaben Amurka, shugabannin kasashen Turai suka fara tunanin yadda dangantakarsu za ta kasance da kasar idan tsohon shugaban kasa Donald Trump ya samu nasara, musamman abinda ya shafi tsaron yankin da kuma harkokin kasuwanci.
Shugaba Macron da Olaf Scholz na Jamus sun dade sun bayyana aniyar ganin kungiyar kasashen Turai ta tsaya da kafafuwarta maimakon dogaro da kasar ta Amurka, musamman a karkashin jagorancin Trump wanda ba shi da tabbas.
Shugaban kungiyar na karba karba Victor Oban na daga cikin na hannun damar Donald Trump da shugaban Rasha Vladimir Putin, kuma yana yawan samun takun saka da takwarorinsa dake yankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI