Shugabannin G20 sun hallara a Brazil don gudanar da taronsu na shekara shekara

Shugabannin G20 sun hallara a Brazil don gudanar da taronsu na shekara shekara

Ƙasashen G20, waɗanda ke riƙe da kashi 85 na tattalin arzikin duniya, su ne su ke ba da kaso mafi tsoka na kuɗaɗen yaƙi da gurɓatar muhalli, kuma babu ƙasar da ta kai su fitar da hayaƙi mai gurbata muhalli a duniya.

A yayin taron yanayi na COP29, babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce dole ne kowace ƙasa ta bada gudummawa a wannan yaƙi, amma kuma don ƙasashen G20 su kasance a kan gaba, duba da cewa su ka fi gudanar da ayyukan da ke gurɓata muhalli.

Shugaba Joe Biden na Amurka tare da takwaransa Xi Jinping na China. Shugaba Joe Biden na Amurka tare da takwaransa Xi Jinping na China. © AP

Wannan ne dai karo na ƙarshe da shugaba Joe Biden na Amurka zai halarci taron na ƙasashe masu karfin tattalin arziki, duk da cewa shugaba Xi Jinping na China wanda ya naɗa kansa a matsayin mai ƙarfin faɗa aji a duniya, kuma mai rajin kare ƴancin ciniki daga ƙudurorin Trump ne zai kasance tauraro a wajen taron.

An dai tsaurara matakan tsaro a harabar taron, wanda ke zuwa kwanaki kadan bayan da aka yi yunkurin tada bom a kotun ƙolin ƙasar da aka zargin masu tsatsauran ra’ayi da kitsa hakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)