Shugabanin kasashe da dama a fadin duniya sun bayyana damuwa da mamaki akan farmakin da magoya bayan shugaban kasar Amurka Donald Trump suka kai a fadar majalisar kasar yayinda ake zaman tabbatar da Joe Biden a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.
Babban sakataren NATO, Jens Stoltenberg ya yada a Twitter da cewa abinda muke gani a Washington abin mamaki ne, dole ne dai a amince da sakamakon zaben da al’umma suka yi.
Firaiministan Birtaniya Boris Johnson ya bayyana lamarin a matsayin ‘abin kunya” inda ya bayyana cewa Amurka ce ke talata demokradiyya a fadin duniya sabili da haka ya zama wajibi ta bi dokokin kasar domin mika mulki lamun lafiya.
A gefe guda kuma shugaban kasar Faransa Eammanuel Macron ya yada a Twitter da cewa abinda ya faru a daren shekaran jiya a Amurka ba “tabi’ar Amurka ba ce”
Haka kuma firaiministan Spain Pedro Sanchez ya bayyana cewa ina bibiyar abinda ke faruwa a Amurka mai tayar da hankali, ina mai yakinin cewa shugaba Joe Biden zai magance matsalar ya kuma hade kan Amurkawa.
Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya yada a Twitter: da cewa " ya kamata Trump da magoya bayansa su amince da hukuncin demokradiyya su daina dagule demokradiyya kasar.