Shugabannin duniya na rige rigen taya Donald Trump murnar nasarar zabe

Shugabannin duniya na rige rigen taya Donald Trump murnar nasarar zabe

Cikin shugabannin da suka aike da sakon taya murnar harda Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya da kungiyar kasashen Turai da kuma shugabannin Gabas ta Tsakiya.

Shugabannin ƙasashen Turan sunyi sauri wajen tura saƙonnin fatan alheri da taya murna da buƙatar haɗin gwiwa, fiye da yadda akayi a baya lokacin da ya lashe zabe a shekarar 2016.

Ga wasu daga cikin sakon da aka aikewa zababben shugaban kasar Donald Trump.

CHINA

Ba tare da bayyana sunan Trump kai tsaye ba, mai magana da yawun ma’aikatar wajen ƙasar Sin, Mao Ning ta ce ƙasar na fatan samun “zaman lafiya” mai ɗorewa tsakaninta da Amurka.

“Zamu cigaba da bibiya da riƙe kyakkyawar alaƙa tsakanin Sin da Amurka a fannin mutunta dangantaka, zaman lafiya, da haɗin kan juna”, inji ta.

Shugaban Rasha Vladimir Putin Shugaban Rasha Vladimir Putin © Maxim Shipenkov / Reuters

RASHA

“Babu ruɗani ko gaba tsakaninmu da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka”, a cewar ma’aikatar harkokin wajen Moscow, tana mai cewa zata yi aiki da sabuwar gwamnatin Amurka tare da bada muhimmanci wajen cimma burikanta akan Ukraine.

Rasha ta ce sharuɗɗanta na tsaida yaƙin da take tsakaninta da Ukraine a bayyane suke a birnin Washington, kuma bazata sauya ba.

UKRAINE

Shugaba Volodymyr Zelensky shi ma ya taya Trump murnar lashe zaɓen da ya bayyana  a matsayin “babbar nasara”, inda ya ce yana fatan shugabancinsa zai kawo zaman lafiya na kurkusa a Ukraine.

“Na yaba da mayar da hankali da Trump yake dashi  na karkafa alaƙa ta hanyar zaman lafiya a fadin duniya”, Zelensky ya faɗa a shafinsa na kafar intanet.

Trump da Netanyahu Trump da Netanyahu © Sebastian Scheiner / AP

ISRAILA

Firaminista Benjamin Netanyahu ya kira nasarar Trump a matsayin wani “babban tarihi da ya dawo” da kuma sabon shafi a Amurka wajen ƙara kulla dangantaka tsakanin Amurka da Israila.

NATO

Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO, Mark Rutte, ya ce dawowar Trump zai taimaka wajen dangatarsu ta ƙara yin kyau, “ ina fatan cigaba da aiki tare dashi  a karo na biyu domin ƙarfafa tsaro ta hanyar NATO”, a cewarsa.

EU

“Mun haɗu ne sakamakon alaƙa mai ƙarfi tsakanin mutanenmu, haɗa kan mutane miliyan 800”, inji shugaban ƙungiyar tarayyar Turai, Ursula von der Leyen a rubutun da tayi a shafinta na X. Mun yi aiki tare kan yarjejeniyar kasuwanci tsakanin manyan ƙasashen duniya da ke cigaba da taimakonmu.

UN

“Majalisar ɗinkin duniya ta shirya yin aikin cikin tsari tare da sabuwar gwamnati domin kawo karshen ƙalubalen dake addabar duniya” a cewar Sakatare-Janar Antonio Guterres.

BIRTANIYA

Firaminista Kier Starmer ya ce kama daga cigaba, tsaro da ƙirƙire-ƙirƙire, nasan cewa kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Birtaniya da Amurka za su cigaba da wanzuwa daga dukkanin bangarorin biyu.

Shugaba Emmanuel Macron Shugaba Emmanuel Macron © Louise Delmotte / AP

FARANSA

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ya shirya tsaf domin aiki cikin mutuntawa da Trump, kamar yadda mukayi kokarin yi cikin shekaru 4 da ya yi mulki.

Ya ce dangantakarsu zata yi la’akari da abinda yake so, amma a bangarensa zaman lafiya da wadata ne.

JAMUS

Shugaban gwamnati Olaf Scholz ya faɗawa Trump cewa munfi kyau idan muna tare.

Dukkan bangarori sun amfana da yarjejeniyar kasuwanci tsakanin manyan kasashen duniya, inji shi. Kungiyar tarayyar Turai da Amurka manyan yankuna masu ƙarfin tattalin arziƙi, wadanda suka ƙara haɗa abokan hulɗarsu a faɗin duniya.

ITALIYA

Firaministar Giorgia Meloni ta miƙa saƙon taya murnarta inda ta ce Amurka da Italiya ƙawayen juna ne, da babu abinda zai raba su.

 Recep Tayyip Erdogan Recep Tayyip Erdogan AP - Richard Drew

TURKIYA

Shugaba Recep Tayyib Erdogan ya taya abokinsa Donald Trump murna, a cewarsa yana fatan alaƙar Turkiya da Amurka zata ƙara ƙarfafa, “yaƙe-yaƙen yankuna da na faɗin duniya, musamman batun Falasɗin da yaƙin Rasha da Ukraine zasu kawo karshe”.

HUNGARY

Firaminista Viktor Orban, na kusa da Trump a Turai, ya kira sakamakon a matsayin dawowa ta musamman a tarihin siyasar ƙasashen yamma.

“Sun yi masa barazanar garƙame shi a gidan yari, an ƙwace masa dukiyoyinsa, an yi yunƙurin ƙashe shi, gaba ɗaya kafafen ƴada labaran duniya a Amurka sun juya masa baya, amma duk da haka yayi nasara,’’ inji shi.

JAPAN

Firaminista Shigeru Ishiba ya ce yana fatan yin aiki kusa-kusa da Trump, domin ƙara ƙarfafa ƙawance da yarjejeniyoyi tsakanin Japan da Amurka.

INDIA

Firaministan India Narendra Modi ya bayyana nasarar a matsayin nasara mai cike da tarihi, a wurin abokinsa Trump.

‘Kamar yadda kayi a shekaru hudun ka na baya, ina fatan mu sabunta alaƙarmu,’ inji sa.

KORIYA TA KUDU

Shugaba Yoon Suk Yeol ya ce ƙarkashin shugabancinka mai ƙarfi, ƙawancen koriya ta kudu da Amurka zata kara ƙulluwa nan gaba. “Ina fatan muyi aiki tare sosai”.

TAIWAN

Shugaba Lai Ching-te ya bayyana cewa yana da ƙwarin gwiwa kan ƙawancen Taiwan da Amurka zai cigaba da wanzuwa a matsayin wani ginshiƙi a yankin.

MEXICO

Shugaba Claudia Sheinbaum ta ce nasarar Trump a zaɓen Amurka ba abu ne na damuwa ba,  duk da barazanarsa akan haraje-haraje da korar baƙin haure.

“Mun tsaya da ƙafarmu, muna da ƴanci, sannan za’ayi alaƙa mai kyau tsakaninmu da Amurka, na yarda da wannan.” Inji ta.

BRAZIL

Shugaba mai sassaucin ra’ayi, Luiz inacio Lula da Silva, ya taya Trump murna da yi masa fatan nasara da cigaba, inda ya ƙara da cewa duniya na bukatar ayyukan hadin kai domin wanzar da zaman lafiya da cigaba.

Sarki Salman bin Abdelaziz Sarki Salman bin Abdelaziz AP

SAUDI ARABIA

Sarki Salman da ɗansa Yarima mai jiran gado Mohammed Bin Salman, sun tura saƙon taya murna ga Trump, inda Sarkin ya bukaci ƙara ƙarfafa alaƙa tsakanin kashen biyu masu ƙawance, wanda kowa ke fatan samun cigaba a kowanne fanni.

QATAR

Sarki Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani, wanda masarautarsa ke da tasiri a yaƙin Gaza, ya ce yana fatan ƙara yin aiki da Trump wajen kawo cigaban tsaro da kwanciyar hankali a yankunan da ma fadin duniya.

MASAR

Shugaba Abdel Fattah al-Sisi yayi fatan dawowar Trump zuwa fadar White House zai samar da tsaro da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

“Ina fatan mu samar da zaman lafiya tare, ƙarfafa hadin gwiwa tsakanin Masar da Amurka”, a cewar Al-sisi.

AFRIKA TA KUDU

Shugaba Cyril Ramaphosa, wanda ƙasarsa zata karɓi shugabancin kungiyar kasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi ta G20, kafin ƙasar Amurka da za ta ƙarba a 2026, ya ce yana fatan cigaba da dangantaka ta kusanci da hadin gwiwa da yarjejeniyoyi tsakanin kashen biyu a bangarori da dama.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu. Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu. © Daily Trust

NAJERIYA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce nasarar Trump ya nuna gaskiya da ƙwarin gwiwar da Amurkawa ke dashi kan shugabancinsa.

“Tare zamu ƙara hada kai a fannin tattalin arziki, samar da zaman lafiya, da kuma magance matsalolin duniya da suka addabi al’umma”, inji fadarsa.

YANKIN TSAKIYAR ASIA

Shugaban Kazakhstan, Kassym-Jomart Tokoyev, ya buƙaci haƙin kai da Trump musamman a fannin tsaro da yaɗuwar makaman nukiliya.

Shi ma shugaba Shavkat Mirziyoyev na Uzbekistan kira ya yi na cigaba da haɗin gwiwar yanki da Trump da kasashe 5 na yankin tsakiyar Asia, na kungiyar “C5+1.

Tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Afghanistan... zai zama cikin haɗin kanmu, inji sa. Sannan kasarmu na jiran ziyara ta musamman daga Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)