Shugabannin BRICS sun bukaci tsagaita wuta a Ukraine da Gabas ta Tsakiya

Shugabannin BRICS sun bukaci tsagaita wuta a Ukraine da Gabas ta Tsakiya

Taron wanda ya samu halartar shugabannin kasashe sama da 20 a Kazan dake kasar Rashar, shi ne mafi girma da aka gani tun bayan mamayar da Putin ya kai wa Ukraine a shekarar 2022.

Wata sanarwar hadin gwuiwar da shugabannin dake halartar taron suka gabatar, ta bayyana matukar damuwarsu da yake yaken dake gudana da kuma rashin zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya tare da yankin arewacin Afirka.

Shugaban China Xi Jinping da na Rahsa Vladimir Putin da kuma Firaministan India Narendra Modi a wajen taron BRICS Shugaban China Xi Jinping da na Rahsa Vladimir Putin da kuma Firaministan India Narendra Modi a wajen taron BRICS via REUTERS - Alexander Kazakov

Sanarwar ta kuma yi Allah wadai da hare haren da Isra'ila ke kai wa kudancin kasar Lebanon tare da bukatar ganin an kare iyakokin kasar baki daya.

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian dake halartar taron a karon farko tun bayan nasarar zaben da ya yi, ya bukaci mahalartar taron na BRICS da su yi duk mai yiwuwa domin kawo karshen yakin Gaza da Lebanon.

Shi ma shugaban kasar China Xi Jinping ya sake kiran samun tsagaita wutar ne, tare da bukatar kawo karshen kashe kashen dake gudana da kuma yin aiki tare domin kawo karshen matsalar tsugunar da Falasdinawa.

Shugaban Rasha Vladimir Poutine lokacin da yake maraba da shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan Shugaban Rasha Vladimir Poutine lokacin da yake maraba da shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan via REUTERS - Alexander Zemlianichenko

A sakon da ya aike, shugaban Brazil Inacio Lula da Silva ya bukaci tsagaita wuta a yake yaken guda biyu dake gudana a Gabas ta Tsakiya da Ukraine.

Silva yace wadannan yake yake guda 2 dake gudana na iya rikidewa su zama na duniya baki daya, saboda haka ya zama wajibi kowa ya bada gudumawa domin kawo karshen su.

Kasar Ukraine ta bayyana cewar matsayin taron ya nuan cewar duniya na tare da kasar a yunkurin ta na tabbatar da zaman lafiya da adalci a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)