Shugabannin ƙasashen Musulmi da na Larabawa na tattauna batun yaƙin Gabas ta tsakiya

Shugabannin ƙasashen Musulmi da na Larabawa na tattauna batun yaƙin Gabas ta tsakiya

Ma'aikatar harkokin wajen Saudi Arabia ta sanar da shirin gudanar da wannan taro tun a tsakiyar watan Oktoban da ya gabata, a wani taron dake goyan bayan samun kasashe biyu tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

Ana saran mahalarta taron su tattauna ci gaba da hare haren da Isra'ila ke kai wa a yankunan Falasdinawa da kasar Lebanon da kuma halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya.

Wannan taron na zuwa ne shekara guda bayan gudanar da makamancinsa a Riyadh wanda kungiyar kasashen Larabawa ta Arab League da ta kasashen Musulmi OIC suka shirya, taron da ya yi Allah wadai da amfani da karfin da ya wuce kima da suka ce Isra'ila na yi.

Cikin shugabannin dake halartar taron harda Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da Firaministan Lebanon Najib Mikati, kuma ana saran taron ya bukaci gaggauta sake kiran tsagaita wuta sama da shekara guda bayan kaddamar da yakin da Isra'ila ta yi, sakamakon harin da mayakan Hamas suka kai mata ranar 7 ga watan Oktobar bara.

Akalla mutane sama da 40,000 suka mutu sakamakon wannan yaki dake ci gaba da gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)