Kodayake bakin dukkanin ƙasashen Larabawan ya zo ɗaya wajen gaggauta yin fatali da aniyar shugaban Amurka ta sauya wa Falasɗinawan Gaza matsuguni, har yanzu ƙasashen sun gaza cimma matsaya a kan wanda ya kamata ya karɓi ragamar jagorancin Zirin da kuma yadda za a samar da kuɗaɗen sake gina shi, bayan ragargaza da Isra’ila ta yi.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce aikin sake gina Zirin Gaza zai laƙume fiye da dala biliyan 53, sakamakon watannni 15 da Isra’ila ta shafe tana kai hare-hare cikinsa da zummar murƙushe mayaƙan Hamas.
A makwannin baya bayan nan shugaba Trump ya tayar da hankalin shugabannin ƙasashen Larabawa da ma wasu ƙarin ƙasashe gami da hukumomin ƙasa da ƙasa, sakamakon shirinsa da ya bayyana na mayar da Gaza ƙarƙashin ikon Amurka, da kuma rarraba al’ummar yankin fiye da miliyan biyu a tsakanin Masar da Jordan.
A ranar 11 ga watan Fabarairu Sarki Abdul na Jordan ya shaida wa shugaban Amurka cewar Masar za ta gabatar da karɓaɓɓen shiri kan makomar zirin Gaza, shirin da ake sa ran taron ƙasashen Larabawan zai tattauna kansa a yau.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI