A wata sanarwa da cibiyarsa ta fitar, ta ce Cater ya mutu ne a gidansa da ke Plains kewa da iyalinsa.
Ɗaya daga cikin ƴaƴansa Chip Cater, ya ce mahaifinsu mutum ne da ke ƙaunar zaman lafiya da fafutukar kare hakkin ɗan adam.
Mahaifina jarumi ne, ba a gare ni kaɗai ba amma ga duk wanda ya yadda da zaman lafiya da kare ƴancin ɗan adam da kuma rashin son kai.
Tun a tsakiyar watan Fabrairun 2023 Carter ya ke kwance ya na jinya a gidansa da ke Plains na jihar Georgia, wani ƙaramin garin da aka haife shi.
Gwamnatin Jimmy Cater dai ta fuskanci ƙalubale a dama, daga ciki akwai yadda Amurka ta gaza kuɓutar da wasu Amurkawa 52 da aka yi garkuwa da su a Iran a shekarar 1980.
Tuni dai shugabannin manyan ƙasashe suka fara mika sakon ta’aziyar rasuwar sa, daga cikinsu akwai Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya da shugaban Faransa da Birtaniya da Brazil da Jamus da Isra’ila da Ukraine da Cuba da Canada da Hungari da dai sauransu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI