Shugaban Rasha ya alƙawarta cikakken goyan bayansa ga ƙasashen Afirka

Shugaban Rasha ya alƙawarta cikakken goyan bayansa ga ƙasashen Afirka

A ganawar da ya yi da wakilan kasashen Afirka a birnin Sochi, shugaba Putin ya yi alƙawarin bayar da cikakken goyon baya ga nahiyar domin ganinta tsaya da ƙafafunta.

Yayin da kasashen yammacin duniya suka juyawa Rasha baya saboda yaƙin da ta ke yi a Ukraine, ƙasar ta yi ƙokarin gina saɓɓin alaƙa da yankin Asia, Afrika da kuma Gabas ta Tsakiya, tare da yunƙurin yaƙi da abinda ta kira mamayar da ƙasashen duniya ke yiwa yankunan ta.

"Kasarmu za ta ci gaba da bayar da cikakken goyon baya ga ƙawayenmu na Afirka a bangarori daban-daban," in ji Putin a jawabinsa da ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov ya gabatar ga sauran ministocin harkokin waje da manyan jami'ai da suka halarci taron.

Shugaban wanda bai halarci taron ba, ya ce alaƙar Rasha da Afirka tana “ƙara karfi” a ƴan shekarun nan.

Wannan taro dai wata dama ce ga Rasha wajen cimma muradinta na ƙara ƙulla danganta tsakaninta da kasashen Afirka, wanda ke zuwa bayan da kungiyar tattalin arziƙi ta BRICS ta gudanar da nata a watan jiya.

Rasha dai ta kasance cikin kasashen da ke taka rawar gani a Afrika tun lokacin da take Tarayyar Soviet, kuma ta cigaba da inganta tasirinta a nahiyar cikin ƴan shekarun nan.

Kasashe 3 na yammacin Afrika da suka haɗar da Nijar, Mali da Burkina Faso sun juyawa Faransa baya tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yiwa shugabannin fararen hula tun daga shekarar 2020, kuma suka koma alakar kut da kut da kasar ta Rashar.

Rasha ta sayarwa wasu kasashen Afirka da makamai wanda kuɗinsu ya zarce dala biliyan 5 a shekarar da ta gabata.

Sojijin hayan Rasha daga ƙungiyar Wagner, yanzu suna taimakawa gwamnatocin Afirka da dama, yayin da masu ba da shawara na Rasha ke aiki tare da jami’an tsaron cikin cikin gida, kana manyan kamfanonin Rasha sun zuba hannun jari mai tarin yawa a nahiyar.

Ga abinda wasu daga cikin ministocin harkokin wajen ƙasashen AfIrka ke cewa yayin taron;

Ƙudirin Rasha na ƴakar ƙasashen yammacin duniya kan iko da suke yi ga ƙasashen Afirka ya fara tasiri ga wasu daga cikin shugabannin yankin.

Rasha ba ta mulkin mallaka, kuma bata taɓa yi ba, a cewar ministan harkokin wajen Mali, Abdoulaye Diop, yayin taron Rasha-Afrika a ranar Asabar.

Sai dai Rasha ta kasance mai mulkin mallaka a cikin ƙarni na 18 da 19 duk da cewa ba’a Afirka ba, amma ta mamaye yankunan Turai, irin su Siberiya, Caucasus da yankin tsakiyar Asia don faɗaɗa ikonta a cikin Eurasia.

Ministan harkokin wajen Burkina Faso, Karamoko Jean-Marie Traore ya ce yarjejeniyar da ƙasar ta ƙulla da Rasha tafi musu wadda suka yi da Faransa tsawon shekaru, sai dai yayi watsi da raɗe-raɗin cewa ƙasar za ta ci gaba da dogaro sosai a kan Rasha.

A wata hira da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, Bakary Sambe, daraktan cibiyar Timbuktu da ke Dakar, ya ɗisa ayar tambaya kan ko fadar Kremlin ta bayar da cikakken goyon baya a alaƙar Rasha da Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)