Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya sanar da jerin manyan na'urorin kera manyan makamai da ake ci gaba da yi, inda kuma ya yi barazanar karfafa rumbun ajiyar makaman nukiliyar.
A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Koriya ta Arewa ta (KCNA), Kim Jong-un, wanda ya yi jawabi taro na 8 na Jam'iyyar Ma'aikatan Koriya da ake gudanarwa a Pyongyang babban birnin bayan shekaru 5, ya ce a shirye yake ya tattauna da Washington, amma ya zama wajibi ga kasarsa ta bunkasa makaman nukiliya da karfafa sojojin ta domin kalubalantar da wata barazana da kiyayya da ka iya fitowa daga Amurka.
A jawabin da Kim ya yi ya bayyana Amurka a matsayar "babbar makiyar Koriya ta Arewa"
Ya kara da cewa ko ma wanene ya kasance shugaban kasar Amurka, kasar za ta cigaba da kasancewa babbar makiyya ga Koriya ta Arewa.
Da yake bayyana cewa kulla sabuwar dangantaka da Amurka ya dogara ne kan ko Washington za ta ci gaba da manufofinta na adawa da kasarsa, Kim ya ce ba za a yi amfani da makaman nukiliya ba sai dai idan sojojin makiya sun fara anfani dasu.