Shugaban Korea ta Kudu Yoon Suk Yeol ya dau alkawalin kare kansa daga matakin tsige shi

Shugaban Korea ta Kudu Yoon Suk Yeol ya dau alkawalin kare kansa daga matakin tsige shi

 

Majalisar kasar Korea ta kudu da ke karkashin ikon ‘yan adawa, wadda ke shirin gabatar da wani sabon kudiri na kada kuri’a a ranar Asabar don tsige Shugaban daga mukaminsa, “ya ​​zama wani dodo mai lalata tsarin mulkin dimokradiyya mai sassaucin ra’ayiShugaban kasar Yoon ya bayyana bacin ran sa  a wani jawabi da ya yi a gidan talabijin.

"Zan yi fada da mutane har zuwa minti na karshe," in ji shugaban masu ra'ayin mazan jiya, wanda farin jininsa ya ragu zuwa kashi 13%.

Tun bayan zabensa a shekara ta 2022 da rata mafi kankanta a tarihin kasar kan shugaban jam'iyyar Democrat, shugaba Yoon bai taba samun rinjaye a majalisar ba.

Da yake bayar da misali da irin matsalolin da ya fuskanta wajen zartar da kasafin kudin nasa, ya bai wa kasar mamaki, inda ya kafa dokar soji ba zato ba tsammani, a daren ranar 3 zuwa 4 ga watan Disamba, kafin daga bisani a tilasta masa soke shi bayan sa’o’i shida bayan matsin lamba daga majalisar da kuma kan titi.

Da kyar ya tsallake rijiya da baya da majalisar dokokin kasar ta gabatar a ranar Asabar da ta gabata, wanda jam’iyyarsa ta cece shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)