Shugaban Korea ta Kudu ya kafa dokar soji don hukunta ƴan adawa

Shugaban Korea ta Kudu ya kafa dokar soji don hukunta ƴan adawa

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa da aka watsa kai-tsaye ta kafar talabijin, shubaban na Korea ta Kudu ya ce, ya ɗauki wannan matakin ne na ayyana dokar soji domin tunkarar barazanar da ke kunno kai daga masu ra’ayin kwamunisancin Korea ta Arewa, dokar da ya ce za ta kawar da irin waɗannan mutanen.

Shugaba Yoon ya ce, jam’iyyar adawa ta kassara harkokin gwamnatin ƙasar ba tare da la’akari da halin da al’umma za su tsunduma a ciki ba, kuma ta yi haka ne saboda matakin da aka ɗauka kan wasu ƴaƴanta da aka tsige su  tare da gudanar da bincike a kansu kan wasu laifuka da suka aikata.

Wannan dambarwar na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar shugaba Yoon ta People Power Party da jam’iyyar adawa ta Democratic Party ke ci gaba da nuna wa juna yatsa kan kasafin kuɗin baɗi, inda  a makon jiya,  ƴan adawar a majalisar suka amince da zabtare wani gagarumin kaso daga kasafin a ƙarkashin wani kwamitin majalisar, kuma da ma su suke da rinjaye.

Yanzu dai shugaba Yoon ya ce, majalisar tarayyar ƙasar ta zamo wata mafaka ga miyagu, inda suke yin mulkin kama-karya domin gurgunta ɓangaren shari’a da na gudanarwa a ƙasar.

Shugaban ya kuma zargi ƴan adawar a majalisar da share manyan batutuwan da kasafin ya kunsa na ciyar da ƙasar gaba kamar yaƙi da kwankwadon kwayoyi da kuma inganta tsaron al’umma.

Ƴan adawar ne dai ke da rinjaye a majalisar dokokin ƙasar mai kujeru 300, yayin da shugaba Yoon ke zargin su da shirya maƙarkashiyar kifar da gwamtainsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)