Mamnoon Hussain, Shugaban kasar Pakistan na 12 ya mutu yana da shekaru 80 a duniya.
Labaran da kafafan yada labarai na kasar suka fitar na cewa dan Hussain, Arsalan Mamnoon ne ya sanar da cewa mahaifinsa ya mutu a wani asibiti da ke Karachi, inda aka kwashe shekara guda ana jinyarsa.
Hussain da aka haifa a ranar 23 ga watan Nuwamban shekarar 1940 a lardin Agra na Indiya, ya fara rayuwarsa ta siyasa a 1969.
Hussain wanda ya rike manyan mukamai a rayuwarsa, ciki har da gwamnan lardin Sindh, ya kasance Shugaban Kasa na 12 daga shekarar 2013 zuwa 2018.