Kafar yada labarai ta gwamnatin kasar Filipin ta sanar da cewa shugaban kasar Rodrigo Duterte ya amince da sabuwar dokar yaki da ta’addanci.
Kamar yadda kanfanin dillancin labaran kasar Filipin ta rawaito shugaban kasar ya rataba a hannu akan sabuwar dokar yaki da ta’addanci. Dokar ta kunshi tsattasuarar matakai domin kalubalantar ta’addanci da karfin gwiwa a kasar.
Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil adama sun bayyana cewa sabuwar dokar ka iya haifar da take hakkkokin bil adama.