Ismail Heniyye, shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ya tattauna batun 'tsagaita wuta da Isra'ila' tare da jami'an gwamnatin Masar.
Mai ba da shawara kan harkokin yada labarai ga Ismail Heniyye Tahir en-Nunu ya fada a cikin wata sanarwa a shafinsa na sada zumunta cewa, shugaban na Hamas ya yi waya da jami’an gwamnatin na Masar.
A cikin bayaninsa, Nunu ya bayyana cewa Heniyye ya gana da jami’an Masar wadanda ke kokarin dakatar da hare-haren Isra’ila a Gaza.
Ministan Harkokin Wajen Masar Samih Shukri ya fada a taron Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya (UNSC), wanda ya halarta ta yanar gizo a ranar 16 ga watan Mayu, cewa tun farkon rikicin Masar ke tattaunawa da bangarorin biyu domin tsgaita wuta da dawo da zaman lafiya a yankin.
A hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a zirin Gaza tun daga ranar 10 ga watan Mayu, mutane 212, da suka hada da yara 61 da mata 36, sun rasa rayukansu sannan mutane 1,400 sun jikkata.