Shugaban na Faransa Macron ya naɗa François Bayrou a matsayin sabon firaministan bayan kada ƙuri’ar yankan ƙauna da majalisa ta yi wa Firaminista a ƙasar Michel Barnier.
Bayrou mai shekara 73 gogagge kuma sanannen ɗan siyasa ne mai tsakatsakin ra’ayi yana kuma da kyakykyawar alaƙa da shugaban Macron.
Ana ganin cewa gogewarsa a siyasa za ta taimaka wurin daidaita lamurran, kasancewar babu jam’iyya dake da rinjaye a majalisar ƙasar.
Babban aikin da ake ganin Bayrou zai yi shine tattaunawa da dukkanin bangarori daban daban na jam'iyyu domin daidaita lamurra a ƙasar kamar yadda wasu makusantan Macron suka tabbatar.
A baya bayannan aka wanke bayrou daga zargin aikata ba daidai ba da kuɗin ƴan majalisar tarayyar nahiyar turai
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI