Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya taya iyaye maza murnar ranarsu.
Shugaba Erdogan, daga shafinsa na sada zumunta ya bayyana cewa,
"Ina taya iyaye maza murnar ranarsu, ina mai jinjina ga ubanni wadanda suka tallafawa iyalansu tsawon rayuwa kuma suka yi amfani da dukkan hanyoyinsu, lokaci da kuma tanadinsu don makomar 'ya'yansu. Ina tunawa da duk uba da dattijan da suka mutu, musamman ma shahidanmu, tare da yi musu addu'ar samun rahamar Allah. "