A lokacin da shugaban hukumar zaɓen ƙasar Igor Karpenko ke gudanar da taron manema labarai da sanyin safiyar Litinin ɗin nan, ya ce sakamakon zaɓen farko ya nuna cewa shugaba Alexander Lukashenko ya samu kashi 86.8 a zaɓen na jiya lahadi.
To sai dai ƴan siyasar Turai na cewa zaɓen baya da sahihanci, domin an hana kafafen yada labarai masu zaman kansu kawo rahotannin yadda zaɓen ya gudana sannan kuma an tursasa manyan ƴan adawa yin gudun hijira wasu kuma an kullesu a gidan yari.
A lokacin da aka tambayi Lukashenko kan kulle ƴan adawa da kuma tilastawa wasu gudun hijira da gwamnatinsa ke yi, yayin wani taron manema labarai da ya gabatar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa su suka zaɓarwa kansu haka domin a cewarsa babu wanda suka ƙora daga ƙasar.
Shugaban Belarus Alexander Lukashenko da takwaransa na Rasha Vladimir Putin. AP - Alexander KazakovTuni dama amininsa shugaba Vladimir Putin na Rasha ya goyi bayan matakinsa na kulle ƴan adawa.
A wani sako da ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta wallafa a shafinta na X, ta ce anyi wa al’ummar Belarus ƙarfaƙar a zaɓen domin babu yadda za su yi, kuma wannan ranar bakin ciki ce ga waɗanda suka daɗe suna fafutukar dimukaraɗiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI