Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da tsohuwar firaminista Sheikh Hasina ta yi murabus tare da tserewa daga ƙasar biyo bayan boren dubun dubatar ɗalibai.
Gabanin rusa majalisar dokokin da aka yi, sai da ɗaliban na Bangladesh suka yi barazanar sake fita zanga-zanga muddin da ba a aiwatar da matakin ba.
Baya ga rusa majalisar da yayi ne kuma, shugaban na Bangladesh ya sanar da sakin jagorar jam’iyyar adawar ƙasar ta Nationalisat Party, kuma tsohuwar Firaminista Begum Khaleda Zia daga ɗaurin tallalar da ake mata a gida, wadda shafe shekaru tana zazzafar adawa da firaminista Hasina da ta yi murabus.
Kawo ƙarshen jagorancin shekaru 15 na gwamnatin Fira Minista Hasina mai murabus a Bangladesh ya samo asali ne daga zanga-zangar ɗalibai da ke adawa da kason guraben ayyukan yin da aka ware wa iyalan fitattun mutanen da suka jagorancin yaƙin nema wa ƙasar ‘yancin kai a 1971, matakin da marasa ƙarfi ke kallo a matsayin hanyar fifita masu kumbar susa sama da su.
Kimanin mutane 300 suka rasa rayukansu, wasu dubbai kuma suka jikkata yayin zanga-zangar da ɗaliban ƙasar ta Bangladesh suka jagoranta daga watan Yuli zuwa Litinin ɗin da ta gabata, inda a jiyan kaɗai wasu alkaluma suka ce rayukan mutane 109 suka salwanta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI