Shugaban 'yan shi'a a Iraki yi yi kira da a kalubalanci Isra'ila

Shugaban 'yan shi'a a Iraki yi yi kira da a kalubalanci Isra'ila

Muqtada al-Sadr, shugaban kungiyar Sadr a Iraki, ya yi kira da a gudanar da wata zanga-zangar don tallafawa al’ummar Falasdinu kan hare-haren Isra’ila ke kai musu.

A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na sada zumunta, Sadr ya ce,

"Dangane da ɗaga dokar hana fita (matakan Kovid-19), ya kamata a gudanar da jerin gwano don nuna goyon baya ga al'ummar Falasɗinu gobe a Bagadaza da duk sauran biranen. Tutar Falasɗinu ce kawai za a ɗauka a wajan tarukan kuma a kona tutucin Amurka da Isra'ila"

Shugaban 'yan Shi'ar, wanda ke son Iraki da wasu kasashe su yi watsi da matakan da za a bi don "daidaitawa da Isra'ila", ya gode wa mutanen Jordan da Lebanon saboda goyon bayan da suke ba wa Falasdinawa.


News Source:   ()