Shugaban Amurka Donald Trump ya janye ƙasarsa daga Hukumar Lafiya ta Duniya WHO

Shugaban Amurka Donald Trump ya janye ƙasarsa daga Hukumar Lafiya ta Duniya WHO

Shugaban na Amurka Donald Trump ya sanya hanu kan dokokin ne jim ƙadan bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasar Amurka na 47 ranar Litinin.

Karo na biyu kenan da Trump ke fitar da Amurka daga hukumar lafiya ta duniya da kuma yarjejeniyar yanayi ta birinin Paris da aka cimma a shekarar 2015 domin rage gurɓatacciyar iska, kafin Joe Biden ya sake mayar da ƙasar cikinta.

Da yake kare matakin janye ƙasar daga hukumar lafiya ta duniya, Mista Trump ya ce Amurka ke bada kaso 20 cikin ɗari na ƙudin gudanarwarta, amma ta gaza tabuka abin azo a gani, masamman bayan ɓarkewar annobar Corona.

Bayaga dokoki da suka shafi shigar baƙi ƙasar da kuma tsugunnar da ƴan gudun hijira, sabon shugaban na Amurka ya dakatar da duk wani taimakon da Amurka ke bai wa  ƙasashen waje har tsawon kwanaki 90, domin sake nazari a kai.

Minista Trump ya kuma rattaba hannu kan dokar ikon shugaban ƙasa da ke bayyana amincewa da jinsi biyu, wato Namiji da Mace, wanda ya ce suke da tushe da ba’a iya sauyasu.

Waɗannan dai umurni ne na zartarwar da ƙundin tsarin mulki ya bai wa shugaban ƙasa, ba ya bukatar sahalewar Majalisa a kansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)