Donald Trump shugaban na Amurka ya shaidawa manema labarai hakan yayin da ya sanya hannu kan wannan doka a Ofishinsa na fadar White House,y ana mai tabbatar da cewa gaskiya za ta bayyana.
A karshen watan Nuwamba, bayan nasarar da ya samu a kan Kamala Harris a takarar shugaban kasa, Donald Trump ya sake maimaita alkawarinsa na yakin neman zabe na bayyana bayanan karshe da aka ware a matsayin "babban sirri" a cikin taskokin tarihi na Kasa game da kisan gillar da aka yi wa John Fitzgerald Kennedy ("JFK") a watan Nuwamba 22, 1963 a Dallas.
An harbe shugaban Amurka na 35 a kan titi, a cikin motar da ke dauke da shi.
John Fitzgerald Kennedy da Martin Luther King © AP, montage RFIKwamitin bincike na hukuma game da kisan ya kammala a shekara ta 1964 cewa Lee Harvey Oswald, tsohon kwamandan Marine da ya rayu a Tarayyar Soviet.
A cikin Disamba 2022, hukumar adana bayyanan kasa ta fitar da takardu sama da 13,000,amma Fadar White House ta Joe Biden ta hana buga wasu dubbai, saboda matsalar tsaron kasa. A cewar hukumar.
Ɗan’uwan John Fitzgerald Kennedy, Robert Francis Kennedy, ya yi aiki a matsayin Babban Lauyansa. An kashe shi a Los Angeles a ranar 5 ga Yuni, 1968, lokacin da yake kan babban matsayi na lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa na Democrats.
Sanatan na jam’iyyar Democrat ya kammala jawabinsa a Otel din Ambassador lokacin da wani Bafalasdine dan gudun hijira zuwa Amurka ya harbe shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI