Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa duk wadanda suke daukar matakan tada zaune tsaye a kasarsa za su yi nadamar da basu taba yin irinta ba.
Putin, a jawabinsa na shekara ya bayyana cewa zai dauka kwararan matakai akan masu yunkurin shirin tayar da zaune tsaye a kasarsa.
Shugaban kasar Rashan ya bayyana cewa Moscow na daukar matakan inganta hulda tsakaninta da dukkanin kasashe kuma bata taba wuce iyaka a harkokin wasu kasashe ba.
Putin ya yi kuma sharhi akan yaki da kwayar cutar Korona da ake yi a kasarsa inda ya bayyana cewa samar da alluran rigakafin Korona har samfura uku a kasarsa na nuni ga irin kwarin gwiwar kanfunan dake kasar.