Shugaba Macron ya buƙaci a kawo ƙarshen yaƙi a Lebanon

Shugaba Macron ya buƙaci a kawo ƙarshen yaƙi a Lebanon

Shugaba Macron ya yi wannan kiran ne a yayin gabatar da jawabinsa a gaban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin New York na Amurka.

Ku latsa alamar sauti domin sauraren jawabin shugaban na Faransa

A daidai wannan lokaci, akwai yiyuwar rikicin da ake fama da shi a Yankin Gabas ta Tsakiya ya faɗaɗa zuwa wasu ƙasashe, a wannan yanayi ina tausaya wa al’ummar Libanan- Inji shugaba Macron.

Macron ya ƙara da cewa, " An share shekaru da dama, Hezbollah na ƙoƙarin ganin cewa ta jefa Libanan a cikin yaƙi, saboda haka Isra’ila ba ta da zaɓi face faɗaɗa hare-hare zuwa Libanan. Muna goyon bayan yin amfani da hanyoyi na diflomasiyya domnin kare rayukan fararen hula da kuma hana yaɗuwar wannan rikici zuwa sauran ƙasashe".

Babu hujjar da za ta iya haifar da yaƙi a Libanan, saboda haka ne muke jaddada yin kira ga Isra’ila ta kawo karshen farmakin da take kaiwa, kamar yadda muke jaddada buƙatar ganin Hezbollah ta dakatar da hare-hare zuwa cikin Isra’ila.

Kazalika shugaban na Faransa ya yi kira  ga waɗanda ke taimaka wa ɓangarorin biyu su gaggauta kawo ƙarshen hakan.

Wannan na zuwa ne a yayin da yaƙin Gaza ya tsallaka zuwa Lebanon, inda Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta kan mayaƙan Hezbollah, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 500.

Tuni ɗimbin ƴan Lebanon suka fara kaurace wa gidajensu da ke yankin kudancin ƙasar domin kauce wa hare-haren Isra'ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)