Shugaba Lula ya caccaki yan jari hujja gabanin taron G20

Shugaba Lula ya caccaki yan jari hujja gabanin taron G20

Tsarin na jari hujja ya kara tabarbare rashin daidaiton tattalin arziki da siyasa da a halin yanzu ya addabi tsarin dimokuradiyya.

A ranar litinin shugaban na Brazil zai haduwa da shugabannin da suka hada da shugaban Amurka Joe Biden, Emmanuel Macron na Faransa, shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, shugaban China Xi Jinping, firaministan Indiya Narendra Modi da Javier Milei na Argentina, domin halartar taron yini biyu na G20 a Rio de Janeiro.

Shugaban China Xi Jinping da Shugaban Brazil Lula Shugaban China Xi Jinping da Shugaban Brazil Lula © Ken Ishii / AFP

Taron dai zai tattauna batutuwa da dama da suka hada da wanda Lula ke gabatarwa kamar kulla kawancen yaki da yunwa a duniya, harajin manyan masu hannu da shuni da kuma neman yin kwaskwarima ga tsarin Majalisar Dinkin Duniya domin yanke shawara mai zurfi.

"Domin shiga zukatan 'yan kasa, gwamnatoci suna bukatar kawar da gibin da ke kara tabarbarewa tsakanin muryar kasuwanni da kuma muryar tituna," in ji shugaban na Brazil.

Taron kasashen G20 a Brazil Taron kasashen G20 a Brazil AP - Bruna Prado

Yayin da matsayin Lula zai samu goyon baya a wasu bangarori a taron G20, sukar da ya yi da kuma bayyana ra’ayin sa na iya haduwa da adawa daga shugaban Argentina Milei.

 Kalaman na Lula sun yi nuni da raunin siyasar wasu shugabannin kasashe masu tafiyar da mulki a karkashin tsarin dimokuradiyyar da arzikinsu ya ragu a baya-bayan nan, a wani bangare na matsalolin tattalin arziki da masu kada kuri'a ke ganin suna cikin wahala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)