Shugaba Biden na Amurka ya gana da Netanyahu kan rikicin Gabas ta Tsakiya

Shugaba Biden na Amurka ya gana da Netanyahu kan rikicin Gabas ta Tsakiya

Ganawar ta wayar tarho, wadda ita ce ta farko tsakanin shugabannin tun bayan wadda suka yi a watan Agusta, na zuwa ne a dai-dai lokacin da rikici tsakanin Isra’ila da mayaƙan Hezbollah yayi muni, ga kuma zaman tankiyar ya kai ƙoluluwa tsakaninta da Iran, yayin da kuma a gefe guda, babu alamun akwai yiwuwar ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, inda dakarun Isra’ilar ke hanƙoron murƙushe mayakan Hamas.

Babu dai ƙarin bayani kan ganawar ta Biden ta Netanyahu, sai dai ana kyautata zaton ba za ta wuce kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya ba, da kuma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Har yanzu dai ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya na cikin zaman ɗar ɗar, kan farmakin ramuwar da Isra’ila ta  sha alwashin kai wa Iran, kan hare-haren da ta kai mata da makamai masu linzami a makon jiya, waɗanda ta ce na jan kunne ne kan farmakin da  Isra’ilar ta ƙaddamar a Lebanon.

A baya bayan nan ne dai cikin wani faifan bidiyo da aka fitar, ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant ya ce, mummunan martanin da babu kuskure cikinsa za su maida wa Iran, kuma hakan zai faru ne cikin bazata. Sai dai  tuni Iran ɗin ta yi gargaɗin cewa muddin Isra’ilar ta kuskura ta aiwatar da abinda take iƙirari, ko shakka babu mummunan al’amari ne zai biyo baya, abinda kenan ya sake haifar da fargabar ɓarkewar sabo kuma ƙazamin yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)