Shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Ɗuniya na fuskantar gagarumar matsala

Shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Ɗuniya na fuskantar gagarumar matsala

Wannan babban ƙalubale da shirin abinci na Majalisar Dinkin Duniya ke fuskanta na faruwa saboda yadda yaƙin da ake gwabzawa a Sudan ke neman futo da gazawar shirin, kamar yadda wani rahoton da Kamfann Dilancin Labarai na Reuters ya gani ya nuna.

Ayyukan raba abinci ƙarƙashin shirin na Majalisar Dinkin Duniya na fama wurin ciyar da miliyoyin Afirkawa dake cikin yunwa, kasancewar yankin mafi fama da ƙarancin abinci.

Rahoton da reuters ta gani ya haska irin girman matsalar da shirin yaƙi da matsalar yunwa ke fuskanta musamman a yaƙin da ake gwabzawa a Sudan, abinda ya ja shirin ke neman gazawa wurin gudanar da  ayyukansa da kuma rashin samun agaji daga masu bada tallafi.

Rahoton da aka tattara tsakanin watan Uli zuwa Agusta ƙarkashin sashin dake kula da aka ɗorawa alhakin faɗaɗa ayyyukan yaki da yunwa a Sudan da makwaftan ƙasashe, ya yi karin bayanin matsalolin da ake ciki cikin shafuka 5.

Labarin rahoton ya zo daidai lokacin da shirin yaki da yunwa na Majalisar Ɗinkin Duniya ke fama wurin samun biliyoyin dalolin da zai yi ayyuka a wuraren da matsalar rashin abinci tafi ƙamari a duniya, ya kuma zo a lokacin da yake fama da rashin tabbas daga bangaran Amurka da manyan masu bada tallafi.

A Sudan kusan rabin adadiin ƴan ƙasar miliyan 50 ne ke cikin barazanar yunwa yayin da ake tsaka da gwabza yakin basasa da aka fara tun a watan Afirilun 2023.

Mataimakin shugaban shirin yaƙi da yunwa na Majalisar Ɗinkin Duniya Carl Skau bai yi cikakken bayani ba kan batun amma ya faɗawa reuters cewa hukumomin jin ƙai basa cikin shiri lokacin da yaƙin Sudan ya barke don haka za a ɗauki tsawon lokaci kafin iya magance wannan matsala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)