Shirin kawar da talauci a duniya nan da 2030 ba mai yiyuwa bane-Bankin Duniya

Shirin kawar da talauci a duniya nan da 2030 ba mai yiyuwa bane-Bankin Duniya

Babban jami'in Bankin duniyar Axel van Trotsenburg ya bayyana cewar yunkurin rage talauci a duniya ya kusan tsayawa cik, ya yin da shirin su na shekarar 2020 zuwa 2030 ya zama mai wahala saboda matsalolin da aka fuskanta a baya cikin su harda annobar korona da sauyin yanayi.

Jami'in y ace kusan mutane miliyan 700 ne a duniya, ko kum akashi 8 da rabi ke rayuwa a kan kasa da dala biyu da centi 15 kowacce rana, abinda ke nuna tsananin talaucin da suke ciki.

Bankin yace ko da nan da shekarar 2030 adadin ba zai gaza kasa da kashi 7 da rab ba, lura da yadda matsalar ta fi kamari a yankin kasashen dake kudu da sahara.

Alkaluman bakin sun kuma bayyana cewar adadin mutanen dake rayuwa kasa da dala kusan 7 ya kai kashi 44, kuma sune ake kallo a matsayin wadanda suka tsallake shingen talauci.

Bakin ya ce adadin mutanen dake fama da talaucin bai yi wani sauyawa na azo a gani ba tun daga shekarar 1990 saboda karuwar jama'ar da ake samu a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)