Ƙuri’un jin ra’ayoyin jama’a da aka riƙa kaɗawa sun nuna yadda ƴan takarar biyu ke tafiya kusan kunnen doki a sakamakon da aka tattarawa.
Al’ƙaluman cibiyoyin da ke sanya idanu kan zaɓen sun nuna cewa Donald Trump ne ke kan gaba da kaso 58 cikin ɗari na yawan mazan da suka kaɗa ƙuri’ar jin ra’ayin jama’ar yayin da Kamala ta jam’iyyar Democrats ke da kaso 40.
Wataƙila a ce mata sun yi ƴar gida don kuwa sune suka fi marawa Kamalan baya inda ta sami kaso 57 cikin 100 na yawan mata, yayin da Trump ke a kaso 41.
Zaɓen Amurka na bana dai ya zo da wani sabon salo mai rikitarwa da zai yi wuya a iya hasashen wanda zai iya lashe zaɓen ganin yadda ƴan takarar ke tafiya kan-kan-kan.
Ƙididdigar kafar yaɗa labarai ta NBC na nuna cewa a baya Kamala bata da goyon bayan baƙaƙen fata da kuma ƴan yankin Karebiya mazauna Amurka, duk da kasancewarta baƙar fata to sai dai kuma sannu a hankali an ga sauyi a kan haka, yayin da aka ci gaba da yaƙin neman zaɓe.
Ƴan sa’o’i ƙalilan suka rage a sanar da wanda yayi nasara a wannan zaɓe da ke da matukar tasiri ga Amurkawa da kuma tsarin siyasar duniya baki ɗaya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI