Shin ko Afghanistan za ta koma karkashin mulkin Taliban ne?

Shin ko Afghanistan za ta koma karkashin mulkin Taliban ne?

An kashe mutane biyu a wani harin bam da aka kai Kabul, babban birnin kasar Afghanistan.

Kakakin Ma'aikatar 'Yan Sandan Kabul Ferdevs Faramarz ya bayyana a cikin wata sanarwa ga manema labarai cewa, wani bam da aka sanya a cikin wani ofishin kula da gidaje a yankin Kabart na yankin Karte-i Nev ya tashi.

Faramarz ya lura da cewa, fararen hula 2 sun mutu yayin da 4 suka jikkata a harin.
Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin.

Babu wanda ya dauki alhakin galibin hare-haren bam din da aka kai a fadin kasar na kimanin watanni 3.

Yayin da zaman lafiya a Afghanistan ya kasance mara tabbas, ana ci gaba da artabu tsakanin jami'an tsaro da 'yan Taliban.

A cewar bayanan da kamfanin dillancin labarai na Anadolu (AA) ya samu daga hukumomin yankin, kungiyar Taliban ta kame fiye da gundumomi 150 daga cikin 407, gami da cibiyoyinsu. 'Yan Taliban, a daya bangaren, suna jayayya cewa adadin cibiyoyin gundumomi da ke karkashin ikonsu ya zarce 205.


News Source:   ()