Shekaru bakwai bayan da DEASH ta kai Sinjar

Shekaru bakwai bayan da DEASH ta kai Sinjar

Shekaru bakwai sun shude tun lokacin da kungiyar ta'addar DEASH ta kai wa Yazidi hari a Sinjar. Kuma har ila yau, yankin na cigaba da kasance wanda ke fuskantar barazanar yan ta'adda. A wannan lokacin a yankin ba wai daga DEASH ba, ya kasance mai fuskantar kalubale daga kungiyar ta'addar PKK da wadanda ke karkashinsu a Sinjar. A yayinda ba za'a iya sake gina Sinjar saboda ayyukan ta'addanci dake cigaba ba, dubban al'umman Yazidi da suka yi hijira sun kasa komawa matsugunansu. Kodayake an yi yarjejeniya tsakanin Bagadaza da Erbil, kungiyoyi masu dauke da makamai irin su PKK da Hashd al-Shaabi na ci gaba da kasancewa a yankin.

Akan wannan maudu'in mun sake kasancewa tare da Mal Can ACUN manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin siyasa, Tattalin arziki da Hallayar dan Adam wato SETA….

A shekaru bakwai da suka gabata, yayin da kungiyar ta'addar DAESH ta kwace tare da tsoratar da yankuna da yawa a Iraki, Yazidis a Sinjar ya zama makasudin wannan mummunan kungiyar ta ta'adda. Rundunar Peshmerga da ta janye daga yankin a wancan lokacin ne ya baiwa DAESH damar mamaye yankin tare da kashe da yawan al'umman Yazidi da kame wasu don mayar dasu bayi. Duk da dai daga bisani dakarun hadakar kasa da kasa sun gudanar da farmakai da suka tsabtace yankin daga DAESH, an rigaya an barnata yankin tare da jefashi cikin halin ha'ula'i.

Tun bayan ficewar Peshmerga yankin ya kasance inda kungiyar ta'addar PKK ta yada zango. A lokacin da dakarun Peshmerga suka janye daga yankin ne wata kungiya reshen PKK wato HPG ta fara bayyana kanta a yankunan. Daga bisani kuma wasu dakarun suka hada kungiya mai suna YBS suka kuma dauki makamai. Ta amfani da hargitsi a yankin, kungiyar ta nemi kafa tsarin gudanar da mulki mai cin gashin kansa a Sinjar, wanda take ganin yana da kima mai mahimmanci akan iyakokin Iraki-Siriya, da kuma sanya yankin ya yi kama da irin yankin da suka kafa a Siriya.

Yankin Sinjar, wanda Erbil da Bagadaza suka bayyana a matsayin mai yanci, kungiyar ta'addar PKK/HPG ta tilastu da fara ficewa daga yankin sabili da farmakai da Turkiyya ke kaiwa ta sama da kasa. Bayan wadanan abubuwan da ke faruwa, kungiyar ta'adda ta dauki sabon salo kuma ta bar mayakan YBS a baya ta ci gaba da kare tasirinsu a yankin. Ala kulli halin, PKK da kungiyoyin dake karkashinta na cigaba da mallakar yankunan tun daga Hanasir zuwa iyakokin Siriya da ma yankuna masu tsaunuka a Sinjar.

Matsin lambar sojan Turkiyya da kwararan matakan diflomasiyya kan kasancewar kungiyar ta'adda ta PKK a Sinjar ya haifar da tattaunawar Sinjar tsakanin gwamnatin Iraki da gwamnatin Kurdawan arewacin lraki, wanda ya kai ga sanya hannu kan yarjejeniyar Sinjar a ranar 9 ga watan Oktoba, 2020, wanda aka yi hasashen fitar da dukkan haramtattun 'yan bindiga da sauran kungiyoyi daga Sinjar. Sai dai ba'a dauki kwararan matakan soja domin tabbatar da yarjejeniyar ba. Ita kuwa PKK ta kalubalanci yarjejeniyar da aka yi tsakanin Bagadaza da Erbil tare da kuma yin hadin gwiwa da Hashd al-Shaabi yankin ya ci gaba da kasancewa inda tutan YBS ke kadawa.

A karshe dai, a yayinda ba za'a iya sake gina yankin saboda cigaba da katutun da kungiyar ta'addar PKK ke yi a yankin Sinjar ba, dubban al'umman Yazidi da suka yi kaura daga yankunansu sun kasa komawa matsugunansu. Domin dai inganta siyasa, tattalin arziki da tsaron Yazidi ya zama wajibi a dauki matakan kauda dukkan kungiyoyin ta'addanci da burbudinsu a yankin Sinjar.

 

Wannan sharhin  Mal Can ACUN ne manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin siyasa, Tattalin arziki da Hallayar dan Adam wato SETA dake nan Ankara babban birnin kasar Turkiyya. Ku huta lafiya.

 


News Source:   ()