Shekara na goma da fara yakin basasa a Siriya

Shekara na goma da fara yakin basasa a Siriya

A cikin wannan maudu'in akan rikicin kasar Siriya  mun kasance tare da Dkt. Murat Yesiltas Daraktan harkokin tsaro a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam wato SETA.

 

An kwashe shekaru goma ana tafka yakin basasa a kasar Siriya har ila yau ba a cimma wata mafita ba. Dubun dubatan Siriyawa sun rasa rayukansu inda kusan miliyan 7 suka rasa matsugunansu tare da tilastuwa daga ficewa daga kasar; lamarin da duniya ta rungumewa hannu ta tsura ido. Har ila yau dai tarzomar da al'umman kasar suka fara a watan Maris din shekarar 2011 domin kalubalantar cin zarafin gwamnatin Bashar Asad na ci gaba. Kawo yanzu dai hadi da Majalisar Dinkin Duniya, kungiyoyin kasa da kasa, Tarayyar Turai da Amurka sun kasa samar da mafita ga rikicin kasar. Su kuwa Rasha da lran sun kara sanya dagule rikicin kasar ne kawai.

Kasa tilo da ta kasance ta na iya kokarinta game da Siriyawa ita ce Turkiyya. Shugaba Erdogan ya wallafa wata kasida mai taken "demokradiyya, ýanci da kare hakkin dan Adam" inda ya yi kira ga bayar da gudunmowa ga kasar Turkiyya domin magance rikicin kasar Siriya. Turkiyya na daukar nauyin miliyoyin Siriyawa a kasarta inda kuma take yaki da ta'addanci da suka hada da Deash, lamarin da ya bata damar kakkabe yan ta'adda daga yankin da kuma kafa sansanin tsaro.

Yayinda Washington ta kasa samawa Siriya mafita a cikin tsawon shekarun nan a halin yanzu ta na kuma neman wani sabon salon da za ta dauka. Siriya dai za ta kasance maaunin ikirarin shugaban kasar Amurka na jamiyyar Democrat Joe Biden akan 'demokradiyya da kare hakkin dan Adam " Akan hakan jawabin shugaba Erdogan a bayyana suke da yake bayyana cewa matukar Biden zai cika akawarin da ya yi a lokacin yakin neman zabe na kawo karshen jidalin da Siriya ke fuskanta dole ne ya yi hadaka damu. Idan gwamnatin Biden ta taimakawa sassan kungiyar ta'addar PKK wato YPG dake Siriya za ta maimaita irin kuskuren da gwamnatin Obama ta aikata.

Kiran da shugaba Erdogan ya yi bai kasance ga Amurka kawai ba. Ya kuma kasance a daidai lokacin da Tarayyar Turai za ta gudanar da taron koli. Babu tabbas dai ga irin sallon tsarin da Turai za ta kaddamar akan Siriya. Ba don matakan jin kai da Turkiyya ta dauka a Siriya ba da yanzu tsarinta ya zama irin na masu tsaurarar ra'ayi da ya kusa mamaye dukkanin manyan biranen kasashen Turai.

Ya dai zama wajibi ga kasashen yamma da su kalubalanci hare haren rokokin Rasha da YPG ke kaiwa a Arewacin Siriya. YPG ta kai hare hare 224 a yankin da aka kaddamar da tsaro. Daga cikinsu 64 da motocin bama bamai, 64 da YEP, 51 da wasu makamai, 19 hari ta sama, 9 kuma da roka.

A yankin da Ankara ke sanya ido a Siriya akwai Siriyawa miliyan 4-5. A cikin kasar Turkıyya kuma akwai akallan Siriyawa miliyan 4 da aka baiwa mafaka. Hakan na nuni ga kamatan bayar da gudunmowa a yankin da aka samar da tsaro a Siriya. Matakan Ankara wajen samar da tsanaki a Siriya lamari ne da zai amfani Turai, kungiyar YPG ba za ta taba daukar matakan kare maradun Siriya ba.

A yayinda shekara na goma ke karewa da fara rikicin kasar Siriya kawo yanzu babu wata mafita da za a iya cewa akwai akan rikicin kasar. Rikicin Siriya da ya kasance rikici mafi muni a karni na 21 idan ba a kawo karshen sa ba babu tabbacin za a samu sukuni a yankin.

Wannan sharhin Dr Murat Yesiltas Daraktan harkokin tsaro a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam wato SETA dake nan Ankara babban birnin kasar Turkiyya. Ku huta lafiya.


News Source:   ()