Sharuɗdan da ke ƙunshe a yarjejeniyar Isra’ila da Falasɗinawa

Sharuɗdan da ke ƙunshe a yarjejeniyar Isra’ila da Falasɗinawa

Wasu daga cikin sharuɗɗan da ke ƙunshe a wannan yarjejeniya sun ƙunshi cewa dole Isra’ila ta janye da tazarar mita 700 ko kuma ƙafa dubu 2 da 297 daga cikin Gaza.

Haka zalika Isra’ila za ta saki fursunonin Falasɗinawa dubu 20 ciki har da wasu 250 da ke fuskantar ɗaurin rai da rai.

A gefe guda Hamas za ta saki fursunonin Isra’ila 33, yayinda Isra’ilar za kuma ta bude iyakar Rafah da Masar cikin kwanaki 7 na farkon faro wannan yarjejeniya.

Bugu da ƙari Isra’ilar za ta fara janye dakarunta daga iyakar Gaza da Masar wato Philadelphi ta yadda za a kai ga janye ilahirin dakarun a rukunin ƙarshe na wannan yarjejeniya.

Nasarar cimma wannan yarjejeniya na da nasaba da matsin lambar gwamnatin Amurka mai jiran gado da ta nemi lallai a cimma yarjejeniyar gabanin rantsar Donald Trump.

Tsawon watanni 15 aka shafe Isra'ilar na ruwan bama-bama a sassan Gaza baya ga wasu yankuna na yammacin kogin Jordan, wanda masana ke kallon yaƙin a matsayin mafi laƙume rayukan jama'a da duniya ta gani a shekarun baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)