Sharhi akan yaki da ta’addanci da Turkiyya ke gudanarwa

Sharhi akan yaki da ta’addanci da Turkiyya ke gudanarwa

Turkiyya na ci gaba da yaki da kungiyoyin ta'addanci musanman PKK a farmakanta da ta kaddamar na Kambori Walkiya da Tsawa a arewacin lraki, inda kawo yanzu ta yi nasarar magance mambobin kungiyar har 150. Ana hasashen cewa a bazarar nan rundunar sojan Turkiyya za ta fadada yaki da ta'addanci da take yi a yankin. Haka kuma kasar na fatattakar yan ta'adda a fadin kasar inda ta magance shugabaninsu da dama tare da hadin kan kungiyar leken asirin kasar ta MIT.

 

Akan wannan maudu'in mun sake kasancewa tare da Mal Can ACUN, manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa,  Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam wato SETA..

A tsarin samar da tsaron kasar Turkiyya kasar ta dauki tsawon lokaci tana kalubalantar kungiyar ta'addar pkk a iyakokin lraki da Siriya. Haka kuma kasar ta dauki kwararan matakan yaki da kungiyoyin ta'addanci cikin gida, dukkan wadanan matakan cike da waje ana kaddamar dasu ne lokaci guda. Hakan ya sanya kasar karya kashin gwiwar kungiyar ta'addanci a cikin kasar inda kuma ta magance kusan 250. Wannan na nuna irin gagarumin nasarar da kasar ta samu a yaki da ta'addanci. Musanman bayanin da ministan harkokin cikin gida Suleyman Soylu ya yi dake nuna cewa ana kusa da karasar da dukkan yan ta'addar dake kasar, lamari ne dake nuna cewa ba za'a samu wasu sabbin yan ta'adda ba, bayan wadanda aka magance.

Haka kuma a daidai lokacin da dakarun kasar ke fatattakan yan ta'adda a lraki da Siriya, hukumar leken asirin kasar ke kokarin magance shugabaninsu a ciki da waje. A bisa wannan tsarin an magance shugabanin yan ta'adda da dama. A yan kwanakin nan an yi nasarar magance dan ta'adda mai suna Sofi Nureddin wanda ke ikirarin jagorantar kungiyar ta'addar PKK a Siriya. Haka kuma,  a Dohok dake kusa da Gara an magance yan ta'adda hudu ta amfani da jirage marasa matuka. A halin yanzu ana daf da tarwatsa masu gudanarwar kungiyar, musanman yadda aka yi nasarar magance da yawa daga cikin masu tsare-tsarensu.

Turkiyya dai ta cimma wani matakin nasarar da ba ta taba kaiwa ba a fagen yaki da ta'addanci. Ta ko wace fanni,  ya Allah a fanni siyasa,  gudanarwa ko kuma a fannin matakan rundunar sojin kasar da kuma ma na hukumar leken asiri hakar Turkiyya ta cimma ruwa a yaki da ta'addanci. Nasarar da Turkiyya ta samu na kara tabbata akan irin namijin kokarin da kanfunan tsaron kasar ke yi da kuma ma yadda ta fara fitar da kayan tsaro zuwa kasashen ketare. A cikin yan kwanakin nan Turkiyya ta yi yarjejeniyar fitar da makamin tsaro kirar TB2 na dala miliyan 400 zuwa kasar Poland wacce mamba ce ta nahiyar Turai da NATO. Dukkan wadanan nasarorin na nuna irin gagarumin tasirin makaman da Turkiyya ta kera cikin gida da kuma shirin cigaba da ingantasu.

Wannan sharhin Mal Can ACUN ne daraktan harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa,  Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam wato SETA dake nan Ankara babban  birnin Turkiyya. Ku huta lafiya..


News Source:   ()