Sharhi akan halin da ake ciki a Afghanistan

Sharhi akan halin da ake ciki a Afghanistan

Gwamnatin Afghanistan ta amince ta tattauna da Taliban don mika mulki.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Afghanistan ta sanar da cewa za a fara tattaunawar mika mulki bayan da Taliban ta fara shiga babban birnin Kabul.

Mataimakin ministan harkokin cikin gida Janar Abdul Sattar Mirzakval ya yiwa mutanen Kabul jawabi ta bidiyon da ya yada a shafinsa na Twitter.

"A matsayina na mataimakin ministan harkokin cikin gida na Afganistan, na umarci dukkan jami'an tsaro, dakaru na musamman da sauran ma'aikata da su ci gaba da ayyukansu a wurare daban -daban don tabbatar da tsaron birnin, ya kara da cewa kada kowa ya damu a halin yanzu babu matsalar tsaro a birnin" 

A gefe kuda kuma masana ba bayyana cewa, rikicin Afghanistan na ci wa mata da kananan yara da suka rasa muhallinsu tuwo a kwarya, in ji Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.

Hukumar ta bayyana cewa, “Mun damu musamman game da tasirin rikicin dake tasiri akan rayuwar mata da‘ yan mata. Kusan kashi 80 wato kaso ɗaya cikin huɗu al'umman Afghanistan miliyan daya da aka tilasta wa yin hijira tun daga karshen watan Mayu mata ne da yara, ”in ji kakakin UNHCR Shabia Mantoo a wani taron manema labarai a Geneva.

Mantoo ta ce kimanin mutane 400,000 ne aka tilastawa barin gidajensu tun farkon shekarar, lamarin da ya kara yawan 'yan Afghanistan zuwa miliyan 2.9 da suka rasa matsugunansu a fadin kasar, in ji Mantoo.

Ta kara da cewa ana ci gaba da fada a cikin larduna 32 daga 34 dake kasar Afghanistan.

A halin da ake ciki a yanzu dai, sojojin Afghanistan a sansanin sojin sama na Bagram, inda fursunoni dubu 5 suke, sun mika shi ga Taliban.

Kakakin kungiyar Taliban Suheyl Sahin ya bayyana cewa suna son mika mulki cikin lumana da shiga Kabul cikin kwanciyar hankali, "An ayyana afuwa ga kowa." 

Ayyukan farko daTaliban ke yi a yankunan da suke ƙarƙashin ikonsu shi ne sakin dukkan fursunonin dake gidajen yarin.

Tun watan Mayu, kungiyar Taliban ta saki dubunnan fursunoni a wuraren da suka kama.


News Source:   ()