An bayyana cewar sakamakon rage karfin garkuwar jikin dan adam da taba sigari ke yi, hakan na kara yawan hatsarin da dan adam ke fuskanta idan ya kamu da cutar Corona (Covid-19).
A aiyukan binciken da masanan kimiyya na jami'ar California suka gudanar game da hanyoyin numfashin dan adam da yadda garkuwar jikinsa su ke, an gano shan taba sigari na hana garkuwar Interferon da ke jikin dan adam aiki yadda ya kamata.
Labaran da jaridar Daily Mail ta fitar ya bayyana cewar binciken ya tabbatar da shan taba sigari na kara karfin kamuwa da cutar har ninki uku.
Dr. Brigitte Gomperts, daya daga cikin wadanda suka gudanar da binciken ya fadi cewar
"Ku yi tunani a ce kamar wasu katangu ne aka gina a tsakiyar hanyar yin numfashi, shan taba na zama kamar farfasa wadannan katangun. Taba sigari na rage karfin garkuwar jiki da kuma bayar da izini ga cutar ta kama mtum."