Masana kimiyya da fasaha sun binciko cewa shan shayi da lemon tsami ita ce hanya mafi sauki na tsawaita rayuwar bil adama.
Kamar yadda masana kimiyya a Amurka suka bayyana, a wani bincike da suka yi sun gano cewa lemon tsami nada sinadarai masu yawan gaske dake taimakawa rayuwar dan adam.
Dangane ga labaran da kafar yada labaran Express ta rawaito, a kasar Misira a zamanin da al'umman kasar sun rinka yawan amfani da lemon tsami domin magance guba.
Binciken ya kara da cewa, lemon tsami na da sinadaran dake magance kwayoyin cuta na bakteriya da biros da kuma kara karfafa ogan dake cikin jikin bil adama.
Daga cikin amfanin lemon tsami dai akwai wanke hanta, musanman yadda yake dauke da sinadaran kalshiyum, maganiziyom, Vitamin C, bioflavonoids da pectin ya na sanya yaki da dukkanin nau'ukan cututtuka a cikin jikin bil adama da kuma kara tsawaija rayuwa.