An sanar da rasuwar shahararren malamin addinin lslama Muhammad Ali As Subuni mai shekaru 91 a gidansa dake Yalova.
Muhammad Ali As Subuni dan kasar Siriya ya yi rubuce rubuce da dama.
Masana Kiwon lafiya da suka ziyarci gidan shehin malamin da zummar duba lafiyarsa suka bayyana rasuwarsa da yan uwansa suka sanar.
Za'a yi janaizar malamin yau bayan sallar Azahar a Masallacin Merkezefendi dake lstanbul akuma binneshi a makabartan yankin.
Subuni ya kasance shugaban majalisar malaman kasar Siriya na tsawon lokaci.
Litattafansa da ya rubuta sun samu karbuwa a Turkiyya da ma a duniyar lslama baki daya. Yana da yar auta da take auren wani saurayi Baturke.