Shugaban majalisar Turkiyya Mustafa Sentop ya mika sakon ta'aziyya ga kasar Indonesiya akan wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar hatsarin jirgin sama a kasar.
Sentop ya yada a shafukansa na sadar da zumunta da cewa,
"Mun yi bakin cikin samun labarin faduwar jirgin sama a Indonesiya lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama. Muna masu addu'ar samun rahamar Allah ga wadanda suka rasa rayukansu"
A gefe guda kuma ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya tattauna da takwaransa na Indonesiya Retno Marsudi.
Cavusoglu ya mika sakon ta'aziyya ga takwaransa Marsudi akan wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar hatsarin jirgin.
A Indonesia, an ba da rahoton cewa jirgin fasinjan "SJ182" na kamfanin jirgin saman Sriwijaya, tare da ma'aikata 12 da fasinjoji 50, ya fado a wani wurin tsakanin Laki da tsibirin Lancang, da ke arewacin babban birnin kasar Jakarta.