Sentop ya mika sakon ta'ziyya akan rasa rayukan hatsarin jirgin kasa a Misira

Sentop ya mika sakon ta'ziyya akan rasa rayukan hatsarin jirgin kasa a Misira

Shugaban Babbar Majalisar Dokokin Turkiyya Mustafa Sentop, sakamakon afkuwar hatsarin jirgin kasa a garin Suhaj da ke kudancin Misira ya mika sakon ta'aziyya ga al'umman Misira ta shugaban Majalisar Wakilai na Misira Hanafy Ali al-Gebaly 

A cikin bayanin da Kodinetan Sadarwa na Majalisar Turkiyya ya yi, Shugaba Sentop ya aike da sakon ta'aziyya ga el-Gebaly.

Sentop, a cikin sakonsa ya bayyana cewa,

"Na samu labari cikin bakin ciki cewa mutane da yawa sun rasa rayukansu kuma mutane da dama sun jikkata a hatsarin jirgin kasa a yankin Tahta na lardin Suhac din Misira. Ina kuma mika ta'aziyata ga mutanen Masar, ina fatan rahamar Allah Madaukaki ga wadanda suka mutu a cikin hatsarin, ina mai fatan hakurin ga iyalansu, da kuma murmurewar gaggawa ga waɗanda suka ji rauni."


News Source:   ()